Matashin Jarimin ya Mitu Tsaka da Tiyatan Sauya-kammni Zuwa Wani Jarimi

 Jarumin fim na Canada ya mutu bayan an yi masa aikin sauya-kamanni guda 12 a jikin 

Dan wasan kwaikwayo na ƙasar Canada, Saint Von Colucci mai shekaru 22 ya mutu bayan ya kashe dala dubu 220,000 a kan yi masa aikin sauya-kamanni guda 12 domin ya yi kama da wani sanannane mai nishadantarwa Jimin.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Jimin memba ne na The Bangtan Boys, BTS, sanannen ƙungiyar mawaka ta Koriya ta Kudu.

A cewar Daily Mail UK, Colucci ya je aikin tiyatar fuskanci domin ya fito a matsayin Jimin a cikin jerin shirye-shirye masu zuwa don dandalin yawo na tushen Amurka.

Jarumin mai shekaru 22, duk da haka, ya samu matsala sakamakon tiyatar muƙamuƙi, kuma an tabbatar da mutuwarsa a wani asibitin Koriya ta Kudu ranar Lahadi.

Colucci ya fara ganin alamun shigar ƙwayoyin cuta a muƙamuƙi 'da aka dasa masa, kuma saboda rurewar jikin, sai aka saka shi cikin wata na'ura kafin ya mutu bayan sa'o'i.


Eric Blake, mai yada labarai na Saint, ya ce dan wasan kwaikwayon ya san hadarin da ke tattare da irin wannan aikin amma ya je aka yi masa.

Post a Comment

Previous Post Next Post