Sojoji Sun Dirar Mikiya Ofishin NDLEA Don Kuɓutar Da Dan Uwansu Da Aka Kama Yana Kwalewa

 wasu zaratan sojoji sun yi dirar mikiya ofishin hukumar NDLEA ta jihar jigawa, suka yi kokarin fidda wani soja da jami’an hukumar suka cafke a samamen da suka kai dabar yan kwaya a jihar ranar Lahadi.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Wani mazaunin kusa da inda abin ya auku ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sojojin da suka kai 10 sun dira ofishin dauke da sanduna da karafuna domin su kubutar da dan uwansu dake tsare a ofishin NDLEA din.

Jami’an NDLEA sun kama wannan sojan ne a wani wuri dake harkallar muggan kwayoyi a da ake kira Gindin Dinya tare da wasu abokan sa faren hula a daidai suna sheke ayar su.

Mutane sun yi cincirindo a kofar ofishin NDLEA din a lokacin da sojojin ke kokarin kubutar da abokin aikin su sai dai kuma a dalilin haka ya sa suka hakura suka fice daga ofishin NDLEA.

Mutane da dama sun yi tir da abinda suka yi inda da yawa da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA suka ce bai dace ace jami’ai irin sojoji su kawo wa hukuma da ke aiki mai kama da nata hari ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post