Video: Ƴan Bindiga sun Shigo Wasu Ƙauyuka Dake Ƙaramar Hukuman Rijau dake Jahar Neja.

 Tun da safe muke ta samun labaran cewa ƴan BANDITS suna kan hanyarsu na shigowa yankunan Rijau, amma hakan baisa mun mai da hankali akan wannan labarin ba, kasancewar an jima hakan bai faru ba.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Bayan fitowa na gida sai naga mutanen ƙauyukan ana ta ɗaukosu a manya manyan motoci, inda ni da idanuna naga wasu harda jini a kafafunansu, haka yasa na tashi dakai na, na bibiyi wannan al'amari.

A zantawa da nayi da wasu daga cikin mutanen ƙauyukan sun tabbatar min cewa waɗannan mutane sunfi mutum ɗari biyar, inda suke ta kora shanayen mutane tare da harbe-harbe, ila yanzu ba musan mutane nawa suka kashe ba, amma sun fita garin Shambo, Inana da Unguwan mai gari boka, sannan suka ratsa ta low-cost suka bi ta makarantar mata dake tsohon garin Rijau.


Muna tunanin kamar suna harin wata kasuwa ne dake wata gunduma da ake kira Sabongarin Ushe, saboda wannan kasuwan kasuwan shanu ne.

Muna kira ga gwamnatin jahar neja da su taimaka su kawo ma wannan ƙaramar hukuma namu mai albarka ɗauki, saboda gaskiya suna neman taimako.


Da alama waɗannan mutane ba suda niyyar bari, kuma sun nuna muna cewa sun fara kenan! 

Allah ya karemu ya kare ƙasanmu baki ɗaya, Allah kuma yaba gwamnati damar ɗaukan mataki.

Post a Comment

Previous Post Next Post