Ambaliyar Ruwa Ta Rushe Gidajen Da Dama A Abuja

 ta rawaito cewa wata Ambaliyar ta lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a safiyar ranar Juma’a.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa, ambaliyar ruwan ta tafi da direban Peugeot 406 mai lamba YLA 681 FS a kan titin Imo da ke cikin rukunin.

An ga mazauna yankin a lokacin da ake yin ruwan sama, suna kokarin ceton rayukansu da kuma ceto dukiyoyinsu bayan da gidaje suka rushe.

Rukunin gidaje na Trademore ya shafe shekaru yana fama da munanan matsaloli na ambaliya da rasa rayuka da dukiyoyi na biliyoyin nairori.

Mazauna wannan katafaren gine-gine duk da haka sun yi gyara a lokacin daminar 2022 domin ambaliya ba ta shafe su ba duk da ruwan sama da aka samu a shekarar.

Mai gidan ya gudanar da aikin gyara wanda ya tabbatar da fadada magudanan ruwa da rushewar ginin da ke wuraren ambaliyar.


Kalli da Wani Mazauni yadauka ta sayanshi Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post