An Kori Minista Saboda Cire Tallafin Man Fetur

HausaChannel rawaito Shugaba Lourenço ya fara wa’adin mulki na biyu a shekarar da ta gabata da zimmar haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

Shugaban Angola João Lourenço ya kori ministan kula da harkokin tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke bayan matakin gwamnati na cire tallafin man fetur. 

Ya maye gurbin Manuel Nunes Júnior, ƙwararren minista kuma farfesa kan tattalin arziki, da gwamnan babban bankin ƙasar, Jose de Lima Massano, a cewar wata sanarwa.

Cire tallafin – wanda Mista Nunes Júnior ya ce an yi ne don rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa – ya fara aiki ranar 1 ga watan Yuni, abin da kuma ya sa farashin man ya hauhawa.


Kalli Video Ministan Yana Kuka😭 Kaitsaye Anan 👇

Tuni zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar mai arzikin fetur, inda ake sa ran za ta ƙaru a ranakun ƙarshen mako.

A ranar Litinin, mutum biyar sun mutu sannan wasu takwas suka jikkata bayan ‘yan sanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a garin Huambo.

Angola na cikin ƙasashen da suka fi arzikin man fetur a Afirka.


BBC Hausa

Post a Comment

Previous Post Next Post