Ansaki Video Yadda ake Cigaban Rushe-Rushen Daren Jiya Lahadi na Gwamnatin Kano

HausaChannel Labarai ta rawaito Yadda Gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da rushe gine-ginen da ke cikin filin Masallacin Idi na Ƙofar Mata.

Motocin Rusau huɗu ne suka ci gaba da rushe gine-ginen Shaguna ɗari da aka yi a cikin filin idin.

Shugaban hukumar tsara birane ta Kano Arch. Ibrahim Yakubu ya shaida wa Freedom Radio cewa abin takaici ne ace an gine filin Babban Masallacin Idi na garin Musulunci.

Ya kuma yi kira ga waɗanda ke da kayayyaki a wuraren da aka sanya wa jan fenti da su gaggauta kwashewa, domin ci gaba da wannan rushe-rushen ya zama dole ba gudu ba ja da baya a cewarsa.


Kalli Video Kaitsaye 👇 Anan 


Post a Comment

Previous Post Next Post