Ɓarayin Kajin Sallah Inspector Sunyi Bayanin Yadda Sukayi Awon Gaba da Kajin Har Cikin Gidan

 Video Barayi Sun Awon Gaba Da Kajin Sallah Na Sefiton Yan Sanda A Zariya 😜

Ana Gaf Da Fara Shan Dafgen Sallah An Shiga Gidan Esfaiton Yan Sanda An Kwashe Kajinsa Sa Shida.

Wani babban Jami’in hulɗa da jama’a na yan sanda ya koka kan yanda wasu mata gari suka kwashe masa kaji a cikin gidansa lokacin suna sharbar bacci.

A wata Anguwa da ake kira Anguwan gwado da ke karamar hukumar sabon garin Zaria jihar Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata cikin dare an bi jami’in dan sanda har gida an masa sata wacce ta girgizashi.

Rahotanni sun nuna cewa jami’in ya sanya abokan aikin sa sun kama wasu daga cikin matasan anguwar an musu duka tare da tsaresu domin bincikar wanda ya aikata hakan.

Sai dai har kawo ranar Litinin gaskiya bata bayyana ba duk a kokarin sa na gano marawon nasa har da yaron cikin sa ya sanya aka kama.

A wani labari kuma da muka samu daga wata majiya mai karfi makwafta dan sanda sun bayyana mana cewa suma an kama yaron gidansu wanda har kawo yau ya na tsare a Area Command PZ.

Makwafta sun bayyana mana cewa yaron nasu bai sa laifi bai ma san an aikata hakan ba amma aka kama shi aka tsare shi duk da zarginsa ake yi.

Mahaifiyar yaron da aka kama ta bayyana mana cewa yaron nata laifin sa kawai domin a gidan dan sandan ya ke kwana kuma a ranar da akayi wannan aika aikan ta bayyana mana cewa baya nan ya tafi farauta kamar yanda ya saba duk dare.

Ta kara da cewa sun gayyaci yaron nata zuwa ofishin yan sanda domin ba da shaida sai dai shi wanda ake zargin ya ce babu in da zai je domin bai aikata laifi ba kuma bai san akan mai zai ba da shaida ba.

Sai dai yan uwan wanda aka kama sun nuna yanda aka keta alfarmar gidan nasu domin yan sanda sun zagaye gidan har da shiga gidan nasu ta bayan gidan duk da an samu dai dai to aka hana su shiga ta nan din.

Bincike ya tabbatar mana da cewa dan san dan an shiga gidan nasa an kwashe masa kaji har shida cikin dare bayan an kama kajin aka yan yankasu a cikin gidan kafin a fitar da kajin.

Kawo yanzu bamu san wani mataki dan sandan zai kara dauka ba duk da iyayen wanda aka kama sun bayyana cewa in har aka gano dansu bai da laifi sai sun shigar da kara domin neman hankin batawa dan nasu suna.

Kalli Video Kaitsaye 👉 Barayin Kajin Inspector 

Post a Comment

Previous Post Next Post