Ibtila’i! Sanata Da Dan Majalisa Sun Mutu a Hadari Hanyar Abuja

HausaChannel Labarai ta rawaito wani Sanata dan ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar Imo akan hanyarsa ta zuwa Abuja domin bikin rantsar da majalisar wakilai ta kasa ta 10 a ranar Talata, sun mutu a wani hatsarin mota.


Video Yadda Haɗarin Yakasance Kaitsaye Anan 👇

Wakilin mu ya tattaro cewa motar da suke ciki ta yi karo da wata motar bas a Agbor da ke jihar Delta.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da mutuwar mutane uku a cikin motar bas, yayin da wasu da suka samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti.

Wani jigo a jam’iyyar da bai so a ambaci sunayensu ba, ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da kodinetocin zababben Sanata mai wakiltar Imo ta Arewa, Patrick Ndubueze da kuma zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Okigwe ta Arewa, Mirriam Onuoha.

Majiyar ta ce, “Mutane uku ne suka mutu yayin da wasu da suka samu raunuka aka garzaya da su asibiti.

Cikin mamatan akwai Maza biyu daga yankin Amaraku da mace daya daga yankin Ogbor duk a karamar hukumar Isiala Mbano.

Da aka tuntubi kakakin jam’iyyar APC na jihar, Cajetan Duke, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

The Punch

Post a Comment

Previous Post Next Post