Jami’an tsaron Saudiyya sun kama mutumin da ya zagi matar MANZON ALLAH (S.A.W)

 Rundunar ‘yan sanda a birnin Riyadh ta tabbatar da kama wani mutumi wanda ya zagi Sayyada Aisha R.A, matar Annabi Muhammad (SAW).

Manjo Khaled Al-kraidis, wanda yanke shine kakakin rundunar ‘yan sandan Riyadh, ya bayyana cewa a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa, an gano cewa bidiyon cin mutuncin ne ga Annabi Muhammad (SAW), haka kuma zagi ne ga uwar muminai, Aisha (R.A).

Bayan kama mutumin an gabatar dashi a gaban kotu domin yanke masa hukumcin daya dace da shi.

An wallafa bidiyon ne a shafukan sadarwa a ranar 10 ga watan Muharram, a lokacin da ‘yan kungiyar Shia suke nuna bakin cikinsu kan kisan da aka yiwa Sayyadina Hussain a lokacin yakin Karbala.

A Musulunci, duka matan Annabi Muhammad guda 11 ana daukar su a matsayin iyaye a Musulunci, a ka’ida ma Musulmai suna so da kuma girmama su fiye da iyayen da suka haife su.

Kotun ta bayyana cewa duk mutumin da aka kama da laifin yada wani abu da ya sabawa addini, ko kuma abinda ya taba darajar addinin Musulunci a idon jama’a, za a ci tarar shi kudi Riyal miliyan 3, wanda yayi daidai da Naira Miliyan 328,548,177 a kudin Najeriya, ko kuma ya yi zaman shekara biyar a gidan yari.


Kalli Video da Shaidan da Kotu ta Bayyana Kaitsaye Anan 👇Post a Comment

Previous Post Next Post