Kayyasa 😭 Sama Da Mutum 100 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Kwara

 Labarai ta rawaito a kalla sama da mutum 100, cikinsu har da wani magidanci da ’ya’yansa hudu ne aka tabbatar da rasuwarsu a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Egbu da ke Karamar Hukumar Patigi ta Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin, lokacin da igiyar ruwa ta kada jirgin da suke ciki ya kuma je ya daki wata bishiya.

Mutanen dai na kan hanyarsu ce daga wani kauye mai suna Egboti a Jihar Neja.

Kimanin gawarwakin mutum 50 ne aka iya ganowa tun bayan faruwar hatsarin.

Wasu majiyoyi daga kauyen sun shaida wa wakilinmu cewa mamatan sun taso ne daga kauyen Kpada.

Majiyar ta kuma ce, “Jirgin na dauke ne da sama da mutum 300 a cikinsa kuma sun dawowa ne daga wajen wani biki.


Kalli Video Kifewar KwaleKwalen Kaitsaye Anan 👇


Mutum 69 daga cikin wadanda suka rasu sun fito ne daga Egbu, 36 daga Gakpan, sai kuma hudu daga kauyukan Kpada da ke Karamar Hukumar Patigi. An kuma ceto sama da 75 daga cikinsu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar hakan.

Sai dai ya ce ba su da cikakkun bayanai, amma ya ji an ce sama da mutum 100 sun rasu, inda ya yi alkawarin ba da cikakken bayani a kan haka da zarar ya samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post