Kotun Majistare Ta Ɗaure Wata Matar Aure Wata 18 acikin Kano

HausaChannel ta rawaito Wata kotun majistare da ke jihar Kano ta yanke wa wata mata mai suna Elizabeth Gift hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari bayan da ya aika mata ta ajiye kudin. a banki.

Mai gabatar da kara, Barista Jamilu Abubakar, ya shaida wa kotun cewa, a watan Afrilu ne mijin nata mai suna Benefice ya aika wadda ake kara a banki domin ta ajiye wadannan kudade a banki, amma sai ta dawo ta ce wasu sun yi amfani da makamai ne suka karbo mata kudin.

Ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa ba a sace mata kudin ba, kuma da gangan ta kai wa wasu mutane da yarjejeniyar cewa za su kara mata kudi.

Wanda ake tuhumar ta amsa laifinta.

Alkalin kotun, Halima Nasir, ta yanke mata hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari tare da umarce ta da ta biya mijinta N2,050,000.

Sai dai alkalin kotun ya ba ta zabin tarar N50,000 ko tsawon watanni 18 a gidan yari.


Kalli Video Firan da Akayi da Ita👇 Kamar Bazata Aikata ba


Post a Comment

Previous Post Next Post