TARON DANGI: Kotu ta bada belin Uba da dan sa da suka gantsara wa wata mata cizo a hanci

 Kotun majistare dake Ota jihar Ogun a ranar Talata ta bada belin Clifford Udouko mai shekara 71 da dansa Ekomen akan kowanen su zai biya Naira 200,000 dalilin kama su da suka yi da laifin gantsara wa wata mata cizo a hanci yayin da suka kaure da fada.

Alkalin kotun A.O. Adeyemi ta ce Udouko da Ekomen za su gabatar da shaidu biyu dake biyan haraji ga gwamnatin Ogun sannan su tabbatar cewa shaidun na zama a wurin da kotun ke da iko.

Dan sandan da ya shigar da karar E.O. Adaraloye ya ce ‘yan sanda sun kama Udouko da Ekomen bisa laifin cin zarafi da tada hankalin Jama’a.


Kalli Video Kaitsaye 👇 Anan 👇


Adaraloye ya ce Udouko da Ekomen sun aikata wannan ta’asa ne a ranar 5 ga Yuni da misalin karfe 4:50 na yamma a layin Ariyo dake Lafenwa, Itele a Ota.

Ya ce a wannan rana Udouku da Ekomen sun kama wata mata mai suna Daramola Olawunmi da duka inda garin duka ne har suka cije ta hanci.

Udouku da Ekomen sun musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Za a ci gaba da shari’a ranar 24 ga Yuni

Post a Comment

Previous Post Next Post