Video Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 a Sokoto Sakamakon Harin Ƙauyuka Jihar

 Rundunar ’yan sanda a jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya, sun tabbatar da kisan mutane a kalla 30, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kaddamar kan wasu kauyukan jihar.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇 Ƴan Sanda da Sauran Jami'ai
Wata sanarwar da ’yan sanda suka fitar, ta ce mutanen da maharan dauke da muggan makamai suka hallaka, mambobin kungiyar ’yan banga ne na karamar hukumar Tangaza. Kuma kafin harin, ’yan bangar sun shiga kauyen Azam, inda suka gargadi mazaunan sa game da yiwuwar kai musu farmaki. Sai dai kuma an samu rashin fahimta tsakaninsu da mutanen kauyen, wanda hakan ya kai ga sun yiwa wasu duka, kuma bayan ’yan bangar sun koma gida ne, maharan suka dira kauyen su, nan take kuma suka hallaka da yawa daga cikin su.

Post a Comment

Previous Post Next Post