Waliyyin Amarya Ya Sace Sadakin Amarya Ana Shirin Daura Aure a Kano

 An tafka abun kunya a wajen wani ɗaurin aure a jihar Kano bayan waliyyin amarya ya sace kuɗin sadaki Waliyyin amaryar dai ya fakaici ido ya ƙunshe kuɗin sadakin amaryar cikin aljihunsa inda ya bar mutane suka yi cirko-cirko ana tunanin ina kuɗi suka shiga Asiri ya tonu ne bayan da aka yanke shawarar a bincike duk mutanen da ke a wajen inda kwatsam kawai sai ga kuɗi a aljihun waliyyin amarya.


Ana zargin wani ɗan'uwan amarya wanda zai bayar da aurenta (waliyyi) da sace kuɗin sadakinta ana dab da ɗaura aurenta a yankin Kurna cikin ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano. Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lokacin da lamarin ya auku, an bar mutane sun yi cirko-cirko suna jiran a ɗaura auren yayin da sadakin ya yi ɓatan dabo. 


Wani mazaunin yankin, Sunusi Dan Mamman, ya bayyana cewa bayan an kwashe dogon lokaci ana jira, mutanen wajen sun amince da a lalube duk waɗanda ke a wajen. 


An gano kuɗin sadakin a aljuhun waliyyin amaryar 

A lokacin ne kwatsam aka yi kiciɓus da kuɗin sadakin a cikin aljihun waliyyin amaryar. Waliyyin ya bayyana cewa bai san yadda aka yi kuɗaɗen suka samu wurin zama ba a aljihunsa 


Bayan an karɓo kuɗin, an kori waliyyin amaryar daga masallacin saboda ba zai iya zama wakilin amaryar ba. Sai aka sanya ƙaninsa a matsayin wanda zai tsaya mata sannan aka ci gaba da ɗaurin auren." Da aka nemi sanin jin ko an cafke waliyyin amaryar bayan an kammala ɗaurin auren, majiyar sai ya kada baki yace babu wanda ke da masaniyar hakan saboda ba a ga motsinsa ba a wajen bayan an kammala ɗaurin auren. 


Kalli Video Yadda Abun Yafaru 😜 Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post