Wata Sabuwa! Wani Ɗalibin JSS 2 Ya Harbe Abokinsa Har Lahira

HausaChannel rawaito wani ɗalibai karamar sakandare ya harbe abokinsa har lahira.

An tattaro cewa yaran biyu suna wasa ne da bindigar mallakin mahaifin wanda ake zaton mafarauci ne.

Matasan dai ana zarginsu da gwada ingancin laya mai hana harsashi tashi ne akan abokin nasa.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇🙆

Jami’an ‘yan sandan shiyya ta Aramoko sun kama wanda ake zargin da mahaifinsa, yayin da aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawa na wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ba a samu cin ta bakinsa ba.

Crimechannels

Post a Comment

Previous Post Next Post