Zargin Cin Hanci $5m: Wasu Kungiyoyi Sun Roki EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Kano.

Kalli Video Kaitsaye Anan 

Wata kungiya mai zaman kanta mai yaki da rashin adalci ta roki Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC da ta yi, bincike da kuma gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje gaban kuliya, bisa zargin karbar cin hancin $5m.

Solacebase ta wallafa cewar kungiyar mai zaman kanta a cikin wasikar mai dauke da sa hannun Babban Daraktanta, Umar Ibrahim Umar, mai dauke da kwanan watan 30 ga Mayu, 2023 kuma aka aika wa kwamandan hukumar ta shiyyar Kano, ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta yi kamar yadda take yi a lokacin da take binciken talakawan Najeriya da irin wannan zargi a kansu

An karanta koken a wani bangare na cewa, ”Za ku iya tunawa cewa a wasu lokutan a shekarar 2018 an yi zargin wasu faifan bidiyo da Malam Jaafar Jaafar babban editan jaridar Daily Nigerian ya wallafa na cewa tsohon gwamnan jihar Kano ya karbi cin hanci daga hannun ‘yan kwangilar har dala miliyan biyar”

‘’Majalisar dokokin jihar Kano ta 8 da ta bankado wannan sirrin, ta kafa kwamitin mutum bakwai da zai binciki laifin da ake zarginsa da shi, amma wannan bincike ya kasance. takaitaccen hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta bayar kan rashin ikon majalisar na binciki duk wani laifin da ya aikata amma saboda kariyarsa a lokacin, babu wani mataki da aka dauka dangane da hakan.

Don haka suke neman shugaban hukumar da yayi mai yiwuwa wajen yin adalci kan koken nasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post