Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mata 23 A Zamfara

 Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mata ashirin da uku a gundumar Damaga da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Alfijir Labarai ta rawaito wani mazaunin yankin mai suna Malam Ahmad Dan Damaga ya bayyana hakan a wata hira da yayi da wakilin Jaridar Alfijir Labarai ta wayar tarho, ya Kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 12:00 na safe, in da wadanda abin ya shafa suka je daji neman itace.

“Don haka kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun gano ashirin daga cikin su yanzu suna cikin zaman talala,” in ji shi.

Ya Kara da cewa ‘yan bindigar sun mamaye garin Talata Mafara shalkwatar karamar hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da ma’aikatan wani kamfanin gine-ginen titi su Goma da aka fi sani da Triacta.

Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Malam Abdulrahman Yusuf a lokacin da ake zantawa dashi ta wayan tarfo ya ce barayin sun mamaye garin ne da misalin karfe 11:00 na daren jiya inda suka fara harbe-harbe, ya ce sun tafi kai tsaye gidan tsohon dan majalisa wakilai mai wakiltar Talata Mafara da Anka Hon. Kabiru Classic.

Sojoji sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar bayan sun shafe awa daya da rabi suna aiki a garin.

Sai dai a kokarin samun martani daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP. Yazeed Abubakar abin ya ci tura don ba a iya samun duka layukan wayarsa.

Kalli Video Kaitsaye 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post