Ɗan Kato Da Gora Ya Auri Wata Baturiya Da Su Ka Hadu A Shafin Sada Zumunta

 Wani matashi mai suna Hamman Joda Isa ya auri wata baturiya da a ke kira Diana Maria Lugunborg, an dai sha shagalin bikin masoyan ne a garin Yola da ke karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

HausaChannel Labarai ta rawaito rahotonni sun bayyana cewa Diana ta niko gari ne tun daga kasar Norway zuwa Najeriya domin ta auri matashin dan kato da gorar (vigilante) da su ka kulla soyayya har ta kai su da yarjejeniyar yin aure a shafin sada zumunta.

Idan zaku tuna cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da matan kasashen yankin Turai, su ke tasowa takanas ta Kano don su auri matasa daga yankin Afrika.

Idan za a iya tunawa ko a shekarar 2020 wata ‘yar kasar Amuruka mai suna Janine Sanchez ta zo ta auri wani matashi mai sana’ar aski da a ke kira Sulaiman Isa dan garin Panshekara jihar Kano da ke arewancin Najeriya bayan watanni goma da fara soyayya a shafin Instagram.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post