Gwamna Ya Kori Wasu Sarakunan Gargajiya Guda Shida

 Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar ma’aikata ta karamar hukumar ta amince da korar wasu sarakunan gargajiya guda shida

Alfijir Labarai ta rawaito gwamnatin jihar Bauchi ta hannun hukumar ma’aikata ta kananan hukumomi ta amince da korar wasu sarakunan gargajiya guda shida saboda “hannun su a siyasar bangaranci da sauran munanan dabi’u”.

Sarakunan da abin ya shafa sun fito ne daga masarautar Bauchi da Katagum.

Korar dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren din-din-din na hukumar Malam Nasiru Ibrahim a madadin shugaban hukumar da aka rabawa manema labarai a Bauchi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar ma’aikata ta karamar hukumar ta amince da korar wasu sarakunan gargajiya guda shida a masarautar Bauchi da Katagum.

Hakan ya biyo bayan shigarsu cikin harkokin siyasa na bangaranci, rashin da’a, ta’ammali da dazuzzuka ba bisa ka’ida ba, da sare itatuwa, da almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda wanda ya saba wa ka’idar aikin gwamnati.

“Wadanda abin ya shafa a cewar sanarwar sun hada da, Alhaji Aminu Muhammad Malami, Hakimin Udubo, Alhaji Bashir Kabir Umar Hakimin Azare, Umar Omar, Hakimin Gadiya, da Hakimin kauyen Umar Bani na Tarmasawa duk a masarautar Katagum.

“Yayin da masarautar Bauchi akwai Bello Suleman, Hakimin Beni da Alhaji Yusuf Aliyu Badara, Hakimin Badara.”

Don haka sanarwar ta umurci sarakunan gargajiya da abin ya shafa da su mika wa sakatarorinsu da kuma majalisun masarautun domin nada jami’an da za su sa ido har zuwa lokacin da hukumar za ta nada manyan hafsoshi.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post