Gwamnatin Kano Ta Soke Lasisin Masana’antar Kannywood Da Gidajen Gala

 Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala a fadin jihar

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a da safe.

El-Mustapha ya ce hakan na nufin babu wanda zai ci gaba da yin fim a jihar Kano sai ya sabunta rajista da hukumar.

Wannan soke lasisin ya shafi masu fitowa a fim, da masu shiryawa, da kasuwancinsa.

Su kuma gidajen rawar Gala an dakatar da su nan take har sai an tantance su.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post