Ibtila’i: Video 🙆 Wani Jirgin Sama Ya Fado A Nijeriya

 Wani jirgin sama mallakin sashin koyon tuki na rundunar sojin sama ta Najeriya mai lamba FT- 7NI ya fado kasa a Makurdi babban birnin jihar Benue.

Alfijir Labarai ta rawaito hadarin jirgin saman ya faru ne da yammacin Juma’a 14 07 2023 a lokacin da a ke tsaka da yin atisaye da shi.

Daraktan Hulda da jama’a da yada labarai na rundunar (NAF) Air Commodore Edward Gabkwet ne ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce matukan jirgin su biyu duk sun tsira da rayukansu sannan kuma su na samun kulawa a rundunar sojin sama ta kasar.

“An yi sa’a duk matukan jirgin guda biyu sun kubuta da rayuwarsu daga hadarin jirgin. Bugu da kari ba a samu asarar rai ko daya ba, haka ba a samu labarin hadarin ya haifar da asara ko barnata dukiyoyin alummar yankin da lamarin ya faru ba”, a cewa sanarwar.

Domin samun sahihan labarai daga Al-Manasik Reporters sai ku latsa wajen da a ka rubuta follow ko kuma ku ziyarci tashar talbinjin ta Al-Manasik Hausa TV a kan YouTube don ku sha kallo.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post