Kungiyar Biyafra (IPOB) Sun Saka Dokan Zaman Gida Ajihar tayi Asarar 10B inji Gwabna

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya koka, yana mai cewa zaman gida da wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) ke yi a yankin Kudu maso Gabas, yana janyo jihar ta yi asarar sama da Naira biliyan 10 a duk ranar Litinin.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan ya bayyana hakan ne a Enugu, a wani taro da ya yi da shuwagabannin kananan hukumomin jihar.

Ya ce ana yin asarar kudin ne saboda ayyukan tattalin arziki da aka hana kowacce ranar Litinin saboda dokar zama a gida ba bisa ka’ida ba.

“Yana da mahimmanci a gare mu mu fahimci alaƙar da ke tsakanin talauci da wannan abin da ake kira zaman-gida.

Duk ranar Litinin da muka zauna a gida, muna asarar sama da Naira biliyan 10 daga ayyukan tattalin arzikin da ya kamata mu samu a jiharmu,” in ji Mbah.

A cewarsa, tunanin rashin tsaro da zaman gida ke haifarwa zai kawo cikas ga shirin gwamnatinsa na tafiyar da tattalin arzikin jihar daga tattalin arzikin da ke tafiyar da harkokin gwamnati zuwa tattalin arziki mai zaman kansa.

Ya ce ba za su taba barin wadanda ba a zabe su ba, su rika ba su umarni.


Kalli Video Kaitsaye 👇👇


Post a Comment

Previous Post Next Post