Wani Matashi na Shirin Yin Wuf da Matar Matarsa Bayan Mutuwar Matar

 Wani mutum ya nemi surukarsa mai shekaru 57 ta aure shi bayan matarsa ta mutu tana da shekaru 34 Mutumin mai shekaru 46 ya rasa matarsa bayan ta haifa masa yara uku kuma a yanzu yana shirin sake aure Ya ce baya son kawo wata daga waje cikin gidansa, amma wasu na kallon shirinsa na auren uwar matarsa a matsayin haramun 

Wani magidanci na neman auren surukarsa (uwar matarsa) shekaru biyu bayan mutuwar matarsa. A labarin da Azuka Onwuka ya wallafa a Facebook, mutumin ya ce gwanda ya auri mahaifiyar matarsa sannan ya guji kawo wata daga waje. 

Matar mutumin ta mutu tana da shekaru 34, inda ta bar yara uku, maza biyu da mace daya. Mutumin wanda yanzu shekarunsa 46 yana neman auren mahaifiyar matarsa wacce ke da shekaru 57 a duniya. 

Yayin da neman auren ya haddasa cece-kuce, mutumin ya dace cewa shine abun da yake so. Karanta labarin: 

Wani mutum (an boye sunansa) ya rasa matarsa bayan sun haifi yara uku (maza biyu da mace daya). Matarsa ta mutu tana da shekaru 34 a duniya. Shekaru biyu bayan nan, yana son auren uwar matarsa mai shekaru 57 kuma bazawara. Shekarunsa 46. Ya ce baya son karin yara ko auren wata daga waje wacce za ta iya raba shi, ko muzguna wa yaransa. Wasu dangin iyalin biyu sun goyi bayan shawarar yayin da wasu ke adawa da hakan.


Jama'a sun yi martani 

Uchechukwu Damian Ononachi: 

Baya bukatar auren uwar matar, sai dai idon daman suna soyayya. Abun da yake bukata shine neman matar ta dawo zama da su sannan ta kula da yaransa. Auren surukar ba daidai bane.

 

 Kalli Cikakkiyar Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post