Wasu Barayin Wayoyin Lantarki Na Ƙarƙashin Kasa Su 3, A Filin Jirgin Sama – FAAN

 Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane uku da ake zargin barayin wayoyin lantarki na karkashin kasa ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.

Alfijir Labarai ta rawaito a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, daraktan hulda da jama’a na hukumar ta FAAN, Abdullahi Yakubu-Funtua, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a makarantar horas da hukumar a ranar Juma’a.

Yakubu-Funtua ya ce tawagar jami’an ‘yan sintiri na sashen binciken laifuka da leken asiri na hukumar tsaro ta jiragen sama (CII), da rundunar hadin guiwa ta soja (JMTF) ne suka cafke wadanda ake zargin.

“An kama Biyu daga cikin wadanda ake zargin ne da misalin karfe 03:52 na yau a yayin da suke tono da yanke waiyoyin lantarki da ke hada MMIA zuwa tashar cikin gida (MMA),” in ji sanarwar.

Dubun barayin zaunen masu sayen kayan a Kasuwar Arena, Oshodi, ta cika suma da misalin karfe 05:56, a tashar Hajj Cargo Terminal sakamakon bayanan da sauran mutanen biyu suka bayar.

“Binciken da ake ci gaba da yi ya nuna cewa an yanke wa daya daga cikin wadanda ake zargin hukuncin daurin kwanaki 28 a gidan yari saboda irin wannan laifin, a wani lokaci a watan Afrilu, 2022 da ya aikata.

“A yanzu haka jami’an hukumar FAAN ta jiragen sama (AVSEC) suna kan yi wa wadanda ake zargin tambayoyi bayan an mika su ga ‘yan sanda domin a gurfanar da su a gaban kotu.”

A ranar 21 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta ruwaito cewa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kama wasu da ake zargi da aikata irin wannan aika aika.

Kafin haka dai FAAN ta sanar da cewa wasu da ake zargin barayi ne suka dauke na’urorin hasken wutar lantarkin da aka sanya kwanan nan a titin cikin gida (18L/36R) na MMIA a Legas.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post