Al’umma Sun Daka Wawaso A katafariyar Ma’ajiyar Kayan Rage Radadi

 Mazauna garin Yenegoa na jihar Bayelsa da dama sun bankara tare da kutsawa wani rumbun ajiyar kayan rage radadi, inda suka kwashe kayan abinci da aka tanadar wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022

Alfijir Labarai ta rawaito katafaren runbun ajiyar da ke kan titin Isaac Boro a babban birnin jihar ne aka dakawa wawar.

An yi awon gaba tare da wawure kayan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai kan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Cire tallafin ya haifar da tashin gwauron zabi na man fetur, wanda hakan ya sa farashin kayan masarufi ya tashi.

Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi alkawarin samar wa ‘yan Najeriya kayayyakin jin kai domin dakile illolin cire tallafin man fetur.

Sai dai ba a bayyana ko kayan agajin da aka wawashe a Yenagoa na cikin abubuwan da aka alkawarta ba.

Bayanai na cewa wasu kayayyakin abincin da ke cikin ma’ajiyar sun kare, amma hakan bai hana mazauna garin yin awon gaba da su ba.

Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su daina korafi, ya ce dole ne Najeriya ta yi ‘yan canje canje mai wahala’ domin a mutuntata a tsakanin kasashe.

Kalli Video daukan waya Kaitsaye Anan 👇Post a Comment

Previous Post Next Post