Barin Warin Takalmi Ya Fallasa Wani Kasurgumin Barawon Gannareto

 Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Nura Abubakar mai shekaru 24 mazaunin unguwar Gada a karamar hukumar Kazaure ta jahar, bisa zargin sa da satar Injin Generata.

Alfijir Labarai ta rawaito tun a ranar 12 ga watan Augusta 2023, wani mai suna Musa Adamu ya yi korafi a ofishin yan sanda, cewar a ranar 7 ga watan Augustan 2023 cikin dare wasu da bai san ko su waye ba sun shiga gidan sa tare da sace masa injin Generata kirar Honda wanda kudin sa yakai naira dubu tamanin da biyar (₦85,000.00k)

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu, ya bayyana cewa sun samu nasarar cafke matashin ne , bayan barin warin takalminsa da ya yi a lokacin da matar mai gidan ta farka daga bacci .

Binciken yan sanda na farko-farko wanda ake zargi ya amsa laifinsa , har ya tabbatar da cewa koda a shekarar 2021 sai da ya taba sace wa, wani mai suna Mallam Musa kudi naira dubu dari da ashirin (₦120,000.00k).

DSP Shiisu Lawan ya kara da cewa yanzu haka suna ci gaba da gudanar bincike kan lamarin , kuma da zarar sun kammala binciken za su gurfanar da shi a gaban kotu dan ya fuskanci hukunci.


Kalli Video Barawon Gannareto Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post