Gwamna Katsina Ya Naɗa Jarumar Kannywood Mukami Rabi’atu Suleiman

 Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya naɗa matashiya mai shekaru 25 ƴar asalin jihar Katsina, mai suna Rabi’atu Sulaiman, a matsayin mai taimaka masa kan sabbin kafafen sada zumunta (Special Assistant on Digital Media) a gwamnatinsa.

Alfijir Labarai ta rawaito matashiyar wadda Gwamna Raɗɗa, ya naɗa tana daga cikin jarumai mata da ake gudanar da shirin Film ɗin “Ƙwana Casa’in, da ita mai dogon zango da ake haskawa a tashar Arewa 24, wacce aka fi sani da suna Khairiyya.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇Haka kuma babu dadewa aka zabeta a cikin shirin manyan mata domin taka rawa a shirin.


Post a Comment

Previous Post Next Post