Kishi: Saurayi Ya Ƙarya Hannun Budurwarsa Saboda Ta Kira Wani Gaye a Waya

 Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tsare wani Abbas Sadiq bisa zargin karya hannun budurwar sa saboda ta kira wani saurayi a waya.

Alfijir Labarai ta rawaito Sadiq wanda mazaunin Unguwar Sheka ne, na fuskantar shari’a bisa tuhume-tuhume guda uku da suka shafi cin zarafin bil’adama, amfani da karfi da kuma haddasa rauni.

Rundunar ƴan Sandan ta shaida wa kotun cewa budurwar ta kawo rahoton cewa saurayin nata, wanda an saka musu rana, ya yi mata dukan tsiya da gangan har sai da ya karya mata hannu saboda tana waya da wani mutum.

Da aka karanta tuhumar da ake masa, ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun, Khadi, Sani Tanimu Sani Hausawa, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Agustan 2023.

Jaridar City & Crime ta kara da cewa bayan yanke hukunci, budurwar da ta ga masoyinta a dakin da ake tsare da ashi a kotun, ta bukaci ta so ta tattauna da shi, inda kuma ta nuna cewa tana son su sasanta.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇Post a Comment

Previous Post Next Post