Rundunar Tsaron Najeriya Ta Fitar Da Adadin Dakarunta Da Aka Kashe

 Manjo Janar Edward Bouba ya ce “‘yan bindigan sun kashe hafsoshi guda uku ne da karin wasu zaratan mayaka 22 bayan kwanton bauna da maharan suka kaiwa dakarun da ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.”

ABUJA, NIGERIA - Hedkwatar Rundunar tsaron Najeriya ne ta bayyana haka a lokacin da ta yi karin haske kan yadda ta yi asarar wasu dakarunta sama da ashirin a jihar Neja.

Video: Jirgin da ke dauke da Sojojin tsaro da ya yi hatsari a Najeriya

Da ya ke magana a taron manema labarai a hedkwatar tsaron kasar, daraktan cibiyar samar da bayanai na irin arangamar da sojojin Najeriya ke yi a sassan kasar daban-daban, Manjo Janaral Edward Buba ya ce abin bakin ciki sun sami koma baya a baya bayannan.

A ranar 14 ga wannan wata na Agusta cikin wasu arangamomi biyu masu alaka da juna, ana farko dai mayakan kasar ne aka musu kwanton-bauna a yankin Shiroro da ke jihar Neja abin da ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

An dai kashe hafsoshi uku da zaratan sojoji guda 22 kana wasu karin mayaka bakwai suka sami raunuka.

Saboda haka wani jirgin saman rundunar sojojin saman Najeriya ya isa yankin don debe gawarwakin mayakan da kuma wadanda suka sami raunuka don kai su jihar Kaduna.

Yayin da jirgin ya tashi a kan hanya ya sami hatsari inda baya ga gawarwakin, su ma sojojin da suka sami raunuka da ma'aikatan jirgin biyu ciki har da direbobinsa biyu duk suka rasa rayukansu.

Mai sharhi kan tsaro, Farfesa Muhammad Tukur Baba, ya shawarci Gwamnatin

 Tarayya da ta dakatar da duk wasu hidimomi don ta tunkari wannan matsalar tsaro gadan-gadan kafin ta watsu zuwa sassan kasar.

Jihar Neje dai sannu a hankali na kara fadawa hannun nau'o'in ‘yan ta'adda daban-daban kamar na ‘yan Boko Haram, mayakan ANSARU, ISWAP da kuma dukkanninsu ke ta fafutukar ganin yin aiki kafada da kafada da ‘yan bindigar da ake kira Barayin Daji


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇Post a Comment

Previous Post Next Post