Sojoji Sun Kwato Mutane 9 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Da Kwato Kudin Fansa A Zamfara

 Sojoji sun samu nasarar karbo mutane 9 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su tare da ƙwato kuɗaɗe da makamai a ƙauyen Gadazaima na jahar Zamfara.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan artabu da ƴan bindigar, inda sojojin suka samu nasarar kashe ‘yan bindiga 10 tare da raunata wasu da-dama a lokacin gumurzun.

Haka zalika, Sojojin sun kama mutane biyu daga cikin ‘yan bindigar, tare da Bindigogi shidda kirar AK-47, Bindiga 1 kirar 1PKT da kuma Magazine 5. Sauran sune bulet 7.62MM mai rawun 20, wayoyin hannu 3, Fanel din Sola 2, Keken ɗinki da Naira Miliyan 2,410,000.

A rahoton da “Rariya ta samu ƴan bindigar sun kashe wata mace wadda tana daga cikin mutane tara da sojojin suka kuɓutar daga hannun ƴan ta’addan.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post