Ta Sake Faruwa! Sojojin Kasar Gabon Sun Yi Juyin Mulki

 Sojoji a ƙasar Gabon dake yankin Tsakiyar Afirka sun ce sun yi wa shugaban ƙasa Ali Bongo juyin mulki.


Alfijir Labarai ta rawaito hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa a karo na uku.

Sun ce sun soke zaɓen da aka yi na ranar Asabar da aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Hukumar zaɓe ta bayyana Mr Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kashi biyu cikin uku na ƙuri’un da aka kaɗa amma ƴan adawa sun ce an tafka maguɗi.

Wannan matakin ya kawo ƙarshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a ƙasar Gabon.

Sojoji 12 sun bayyana a Talabijin inda suka sanar da soke zaɓen tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”.

Ɗaya daga cikin sojojin ya sanar a gidan Talabijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen wannan gwamnatin.”

Mr Bongo ya hau kan mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2009.

Kawo yanzu babu wani martani da gwamnatin Gabon ta yi game da sanarwar juyin mulkin.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇Post a Comment

Previous Post Next Post