Video: Gudanar Da Zanga-Zangar Ƙyamar Cin Hanci A Kotunan Zaɓe Na Kano

 Wasu kungiyoyin fararen hula a Kano sun gudanar da zanga-zangar nuna kyamar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya dabaibaye kotunan sauraren kararrakin zabe.

Alfijir Labarai ta rawaito a makon da ya gabata ne taƙaddama da ɓarke, bayan Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisun tarayya da na jihar Kano, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.

Rahotanni dai sun ambato Mai shari’a Flora Azinge na cewa karo na biyu ke nan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.

Manyan jam’iyyun siyasar jihar guda biyu NNPP mai mulki da APC, babbar mai hamayya a Kano suna nuna wa juna yatsa.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post