Wata Sabuwa! An kashe Sojojin Nijar 17, An Kuma Raunata 20 A Wani Hari

 Ana zargin masu ikirarin jihadi ne suka yi kwanton baunar.

Alfijir Labarai ta rawaito a kalla sojojin Nijar 17 suka rasu sakamakon wani hari wanda ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai shi kan iyakar Mali.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata sanarwa da ma’aikatar tsaro ta kasar ta fitar inda ta ce an yi kwanton bauna kan dakarun ne a garin Koutougou.

Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa baya ga sojojin da aka kashe, akwai wasu sojoji 20 da suka samu raunuka, shida daga cikinsu sun samu mummunan rauni.

Sama da mahara 100 sojojin suka halaka a samamen da suka kai, in ji sojojin.

Rikicin masu ikirarin jihadi ya jefa yankin Sahel cikin wani hali tsawon shekaru, inda lamarin ya yi kamari a Mali a 2012 kafin ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso a 2015.

Rikici a yankin na Sahel ya yi sanadin mutuwar dubban sojoji da ‘yan sanda da farar hula inda kuma miliyoyin mutane suka rasa muhalansu.

Fushi da irin zubar da jinin da ake yi ya tunzara juyin mulki a duka kasashen tun daga 2020, inda juyin mulkin Nijar shi ne na baya-bayan nan wanda aka yi a ranar 26 ga watan a Yuli inda aka hambarar da Shugaba Bazoum.

Kalli Cikakkiyar Video Halin da Ace Cikin akan Iyakar 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post