Aika-Aika: Wani mutum da ake zargi da yin tsafi ya kashe ma’aikata 2 a jihar Bauchi

 Wanda ake zargin wanda ya fito daga kauyen Dankunkuru karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano,

Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Ibrahim Umar mai shekaru 40 a duniya bisa zargin kashe wasu ma’aikata guda biyu a karamar hukumar Gamawa da ke jihar Bauchi.

Wanda ake zargin wanda ya fito daga kauyen Dankunkuru karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, ana kyautata zaton ya kamala yin garkuwa da mutanen biyu, Kabiru Idi ‘mai shekaru 36 da Bato Ali, mai shekaru 18, bisa zargin aikata wani aiki na tsafi a daya daga cikin tafiye-tafiyensa na kasuwanci. zuwa kauyen Taranka dake karamar hukumar Gamawa.

An ce lamarin ya faru ne a watan da ya gabata.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar Damke su ne a ranar 10 ga Satumba, 2023, lokacin da wani Adamu Mohammed, mai shekaru 57, daga kauyen Taranka guda karamar hukumar Gamawa, ta Jihar Bauchi, ya kai rahoto a hedikwatar ‘yan sanda ta Gamawa cewa, Idris da Ali har yanzu ba a gansu ba.

Sanarwar da Kakakin Rundunar, Mohammed Wakil, ya fitar a daren ranar Talata, ta bayyana cewa, binciken da aka gudanar ya gano cewa wadanda ake zargin sun kashe mutanen biyu ne a wani yunkuri na yin kud’i daga gawarwakinsu.

Ya ci gaba da cewa bayan samun rahoton, ‘yan sandan sun tsara wata tawagar da aka tura su wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa, inda daga bisani suka cafke wanda ake zargin.

Sanarwar ta kara da cewa, a wani bincike da aka gudanar a gidan wanda ake zargin, an gano galan roba daya dauke da sinadarai da ake zargin jinin Dan Adam ne.

Ya ce, “A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kashe ma’aikatan guda biyu tare da binne su a wani rami mara zurfi da ke wajen garin, sakamakon haka ne aka bawa jami’in binciken tono gawarwakin daga ramin domin a yi bincike mai zurfi. .”

“bayan kammala binciken gawarwakin likitocin sun tabbatar da cewa sun mutu.”

A halin da ake ciki, rundunar ta mika gawarwakin ga ’yan uwa domin binne su kamar yadda addininsu ya tanada, yayin da ake ci gaba da bincike don gano sirrin da ke tattare da aikata wannan aika-aika.

Sanarwar ta ruwaito kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Auwal Musa Muhammad yayi Allah wadai da wannan danyen aiki, da kuma tabbatar da doka zata yi aikinta, kuma ba za a laminci irin wannan cin zarafin ba.

Click to Watch the Video 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post