Ƴan Bindiga Sun Harbe Mutum 5 A Masallaci 2 kuma Akan Hanya A Jihar Kaduna

 Hakimin kauyen, Malam Abdulrahaman Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shugaban ƴan banga na kauyen na cikin wadanda aka kashe a cikin masallacin.

Alfijir Labarai ta rawaito ƴan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Saya-Saya a Karamar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.

An kashe biyar a cikin masallacin, yayin da sauran biyun aka kashe a wurare daban-daban a yankin.

Rahotanni na nuni cewa Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na dare a lokacin da mutanen kauyen ke yin Sallar Isha’i a wani masallaci da ke yankin, kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Wani mazaunin kauyen mai suna Dan Asabe, ya ce an garzaya da wasu mutanen kauyen biyu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibiti domin yi musu magani

Hakimin kauyen, Malam Abdulrahaman Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shugaban ƴan banga na kauyen na cikin wadanda aka kashe a cikin masallacin.

Ya ce jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda daga garin Ikara da kuma yankin Palgore sun isa wurin da misalin karfe 12:30 na safe, amma zuwa lokacin, ‘yan bindigar sun bar kauyen.

A cewarsa, daya daga cikin wadanda suka samu raunukan harbin bindiga an kai shi asibitin Aminu Kano domin yi masa magani.

Mukaddashin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Mansir Alhassan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa dazuzzukan da ke kusa da su domin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.


Kalli Cikakkiyar Video 


Post a Comment

Previous Post Next Post