An Sake Daka Wawa Kan Motoci 3 Dauke Da Shinkafar Da Za A Raba Tallafi

 Bata-garin sun rika jejjefa wa jama’a shinkafar har sai da motocin suka kare

Alfijir Labarai ta rawaito asu bata-gari sun daka wawa a kan wasu motoci uku da ke dauke da shinkafar da za a raba tallafi a wasu yankunan Jihar Kwara.

Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a yankunan Oja-Oba/Idi-Ape/Isale-Oja da ke Kananan Hukumomin Ilorin ta Gabas da Ilorin ta Yamma.

An kwashe kayan ne wajen misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Juma’a, a dab da ofishin ’yan sanda na ‘C’.

Mutanen dai sun yi wa motocin kirar Toyota Dana kwanton bauna ne, lokacin da suke dauke da kananan buhunan shinkafar masu nauyin kilogiram 10, a kokarinsu na wucewa don zuwa wasu yankunan Jihar.

Shaidun gani da ido sun ce sai da bata-garin suka yi wa motocin karkaf kafin su ranta a na kare.

A cikin bidiyon, an ga bata-garin suna jejjefa wa jama’a buhunan, yayin da su ma suka debi kason su ba tare da wani ya taka musu birki ba.

Bidiyon wawason dai ya karade shafukan sada zumunta na zamani a fadin Jihar.

Mazauna yankin sun ce daga bisani ’yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka yi tambayoyi, kodayake ba su kama kowa ba.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce ba su da masaniya a kan wawason.

Ya ce amma idan ya bincika zai yi masa bayani. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi hakan ba.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post