Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 6 Tare Da Kama Wasu A Mutane 54 A Filato

 Dakarun sojojin rundunar Operation Safe Haven (OPSH), sun kashe wasu masu garkuwa da mutane shida tare da kama wasu ‘yan bindiga a wasu ayyuka daban-daban a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar tace, an kama mutane 54 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, barna a gonakin jama’a, fashi da makami, kera bindiga da safarar miyagun kwayoyi da dai sauransu.

Jami’in yada labarai na rundunar, Kyaftin Oya James, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, sojojin sun kuma kama wasu masu garkuwa da mutane guda uku da kuma wani da ake zargin dan bindiga ne mai suna Dauda Tahiru kan harin baya-bayan nan na karshe da aka kai a kauyen Heipang da ke karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.

“Hakazalika, bayan samun bayanan sirri, sojojin sun gano tare da kama wani shahararren mai kera bindiga wanda ake kira da Nyam, da wani kuma a kauyukan Kwang/Kafanchan na Jos ta Kudu da Jema’a na jihohin Filato da Kaduna.

A yayin samamen, sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, harsashi mai tsawon 7.62mm guda 55, bindiga kirar DICON AK-47 guda daya mai lamba 563706042 da kuma kwalbasar harsashi guda daya.

James ya kara da cewa, sojojin sun kama wasu makiyaya biyu Musa Mamuda da Musa Alhaji da laifin lalata gonaki a kauyen Yagbak da ke Zangon Kataf sannan kuma an kwato shanu 27 a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

Ya kara da cewa, an kama wasu dilolin kwayoyi 41 a Kongo Rasha da ke Jos ta Arewa, an tsare su domin hukumar NDLEA ta ci gaba da gudanar da bincike akansu.

Kalli Cikakkiyar Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post