Hukumar NSCDC sun kama mutum 76 da ake zarginsu ne auren jinsi a Gombe

 Zamu mai da wadannan mutane da suka kama makaranta yadda ba za su samu lokacin aikata muggan aiyukka irin haka ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar Sibul Difens ta NSCDC a jihar Gombe ta bayyana cewa dakarunta sun kama mutum 76 da ake zargi ‘yan luwadi ne a jihar. Shugaban hukumar Mohammed Mu’azu ya sanar da haka ranar Lahadi.

Mu’azu ya ce daga cikin mutum 76 din da aka kama akwai maza 59 da a cikinsu akwai 21 da suka tabbatar wa jami’an tsaron cewa su ‘yan luwadi ne, sannan da kuma da wasu mata masu madigo 17.

Ya ce sun kama wadannan mutane a Duwa plaza dake hanyar Bauchi zuwa Gombe yayin da suke taron tunawa zagayowar ranar haihuwa da daurin auren mambobin su.

Mu’azu ya ce zai mai da wadannan mutane da suka kama makaranta yadda ba za su samu lokacin aikata muggan aiyukka irin haka ba. Daga nan kuma ya ce da zaran sun kammala bincike za a kai su kotu domin yanke musu hukunci.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post