Mutane 8 sun mutu, wasu 10 sun jikkata, a wani mummunan hadari a Abuja

 Akalla mutane takwas ne daga cikinsu a kwai wasu dalibai suka mutu, bayan da wata babbar mota da ke dauke da yashi tayi musu diban karan mahaukaciya a unguwar Mpape da ke kusa da gundumar Maitama a Abuja.

Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 4 na yamma, a daf da tashar masu Keke Napep a kan titin da ke kaiwa zuwa mahadar Mpape.

Wani ganau mai suna Mustapha Aminu ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa motar ta kutsa cikin wasu Keken Napep da wasu motoci, inda akalla mutane 8 suka rasa rayukansu ciki har da dalibai. Aminu ya ce direban da ya ga irin barnar da ya yi ya bar motar ya gudu abinsa.

Lokacin da lamarin ya faru, ina kusa da titin. Ya yi illa sosai lamarin. Ya kashe kusan mutane takwas kamar yadda na kirga, mutane na cewa birkin tirelar ne ya lalaceA wurina, abin da ya jawo faruwar lamarin da farko shi ne wata tayar motar ta fashe, wanda hakan ya rasa iya sarrafa ta.

“Ba wanda ya ji ƙarar horn daga motar, domin a wasu lokuta idan irin wannan lamari ya faru, mutum ya rika jin ƙarar horn daga nesa, sannan mutane kan tsaya daga gefen hanya, wanda yin hakan Daga direban kansa a ceci rayuka da dama.

“Fiye da Keken Napep bakwai da motoci da yawa abin ya shafa. Kimanin dalibai biyu a cikin daya daga cikin kekunan uku sun mutu nan take,” inji shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan sashin na babban birnin tarayya Abuja, Chorrie Mutaa ya ce tawagarsu ta ceto gawarwaki biyar da kuma wasu 10 da suka jikkata.

Ya kara da cewa motoci 13 da suka hada da babbar motar da ta yi hatsarin da babur ne suka yi hatsarin.


Kalli Video Kaitsaye 👇
Post a Comment

Previous Post Next Post